|
Description:
|
|
Wata Kotu a Najeriya ta daure wani malamin Jami’ar Obafemi Awolowo shekaru biyu a gidan yari, saboda samun sa da laifin bukatar lalata da wata dalibar sa kafin ba ta makin jarabawa.
Mai shari’a Maurine Onyetenu tace malamin Farfesa Richard Akindele ya ci amanar da aka bashi, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari. Dangane da wannan hukunci, mun tattauna da Malam Muhammad Hashim Suleiman, da ke koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ga tsokacin da yayi akai. |